Codedwap

Hira ta musamman da Shugaba Muhammadu Buhari

 • Uploaded on 24 Des 2015

  A yayin da ake bankwana da shekarar 2015, wani abu da yafi daukar hankalin wasu 'yan Najeriya shi ne, inda aka kwana, da batun kawo karshen kungiyar Boko Haram a wannan wata na Disamba.

  A hira ta musanman ta yayi da Editan sashin Hausa na BBC Mansur Liman, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce tabbas an karya lagon kungiyar ta Boko Haram, domin a halin yanzu, bata da karfin kaddamar da gagarumin hari, ko karbe wani gari.

  Shugaba Buhari ya ce saboda cin galabarta da aka yi, kungiyar ta Boko Haram ta koma wa amfani da kananan yara, musanman mata a matsayin 'yan kunar bakin wake, kuma ya ce ana daukan matakai na shawo kan hakan.

  Sai dai Mansur Liman din ya fara ne da tambayar Shugaba Buharin ko wadanne hanyoyi ne gwamnatinsa za ta bi, wajen nemo kudaden da za ta aiwatar da kasafin kasar na 2016, ganin cewa shi ne mafi girma dakasar ta taba yi, kuma ya zo a daidai lokacin da farashin mai a kasuwannin duniya ya fadi warwas.

  Channel BBC News Hausa

Codedwap

Download Links

TAGS:

Youtube Hatena . Webry . bd . Tripod . Addto . So-net . Gamer . Google+ . images . ucz . hawaii . nla . dot . bts . ed . dhs . weather